ASHURA: A DAY FOR THE OPPRESSED Print
Written by freezak   
Tuesday, 10 September 2019 14:22

The tenth of Muharram of every year is the day of Ashura, the tenth day in new Islamic calendar. The day of Ashura is historically significant due to the unprecedented tragedy that befell the pure Household of the Holy Prophet Muhammad (SAWA) in the plain of Karbala 61 AH. 

On that fateful day, Husain, Grandson of the Holy Prophet, son of Imam Ali (AS) and Sayyidah Fatimah (AS) was mercilessly slain alongside his family members and a handful of his companions in cold blood by the army of despotic Yazid, son of Mu’awiyyah.

We, the followers of Imam Husain (a.s.), who on the recommendation of other Infallible Imams arrange these sustained mourning sessions, have the same problem. We face tyranny, we face the cruelty of oppressors. But we maintained the event of Karbala; our preachers kept the event of Karbala alive, they kept alive the issue of the resistance of a small group but with immense faith vis-a-vis the powerful but arrogant regime. Shedding tears for martyrs is tantamount to keeping the movement alive. It has been narrated that he who sheds tears, or make others weep, or even sham lamentation and grief, will be rewarded by admission to the Paradise. This is because even he who simulates mourning and lamentation for the event of Karbala, is helping to preserve the movement and uprising that was initiated by Imam Hussain (a.s.) via his martyrdom at Karbala.

This is the reason agents of neo-colonialists prevented these gatherings for lamentation of the Ashura Event. They had studied the circumstances of the nations and knew that they could not reach their aims as long as such mourning sessions and recitation of elegies were held and the cruelties of rulers were revealed and condemned.

They do not know that weeping for Imam Hussain (a.s.) means perpetuation of his uprising and maintaining the fact that even a small number could stand up against oppression. Imam Hussain's decree is that: "Every day is an Ashura and each territory is Karbala!" implies that his movement must be kept alive and active everywhere and at all times. This statement is our manual of action. Just as Imam Hussain (a.s.) stood up and said: "No!" to tyranny, his decrial must be repeated daily and these mourning sessions mean the perpetuation of the negation. Let our children and youth not consider this as a mourning matter, it is not that ours is the weeping nation. 'They (the enemies of Islam) fear these mourning sessions for it is a cry in support of the oppressed. It is an outcry in opposition to the tyrants.

We use this period of mourning to condemn the crimes of the Saudi-led coalition in killing of civilians in Yemen, and other similar atrocities in Syria, Iraq, and Afghanistan. We also condemn the brutal attacks on Palestine by the vicious Zionists of Israel. We abhor the illegal sanctions unilaterally imposed by Trump on the Islamic Republic of Iran.

Here in Nigeria, the Islamic Movement led by Sheikh Ibraheem Yaqoub Zakzaky (H) had been victim of series of machinations, especially by the present government and other past governments through international conspiracy. The massacre carried out by the Nigerian army in Zaria on 12-14 December, 2015 bore many similarities with the inhumane atrocities unleashed on Imam Husain, his family and followers in the plain of Karbala.

In 2016 a federal high court set our leader free, condemning his incarceration as unknown to any national or international law, however Buhari administration refused to obey that court order. Instead it used the Kaduna state government to institute another legal tussle, where trump up charges were slammed against our leader Sheikh Ibraheem Zakzaky. Even in the Kaduna state high court, he was granted medical leave to visit India to regain his daily deteriorating health condition, but the government botched up his medical trip to India last month.

As we mourn Ashura, we urge the federal government to release Sheikh Zakzaky, his wife and hundreds of other still in detention since December 2015 and restore the fundamental human rights of Muslim brothers and sisters of the Islamic Movement in Nigeria.

SHEIKH ABDULHAMID BELLO
Muharram 10, 1441 (September 09, 2019)

 

 


*ASHURA: RANAR WADANDA AKE ZALUNTA*

Ranar goma ga Muharram na kowace sabuwar shekarar kalandar Musulunci ce ranar Ashura. Ranar Ashura tana da gayar muhimmanci a tarihi saboda mummunar musibar da ta auka wa tsarkakan iyalan gidan Annabi Muhammad (SAWA) a falalin Karbala a shekara ta 61H. A wannan rana ne Imam Husain, Jikan Ma’aiki Mai tsira da aminci, dan Imam Ali (AS) da Sayyidah Fatima (AS), aka yi masa kisan gilla tare da dukkan iyalansa da tsirarun mabiyansa a hannun Mujirimi mai mulkin kama-karya, Yazidu dan Mu’awiyyah.

Mu da muke mabiyan Imam Husain (AS), wadanda kuma bisa umurnin sauran Imamai Ma’asumai muke shirya wadannan zaman makokin na Ashura, muna fama da irin matsalar da Imam Husaini (AS) ya fuskanta ne. Muna fama da zalunci da fushin azzalumai ne. Amma za mu ci gaba da raya al’amarin Karbala, masu wa’azinmu abin da suke yi ke nan, suna nuni da cewa jama’a ‘yar kadan wacce take cike da imani za ta iya tsayawa gaban karfafan azzalumai.

Zubar da hawaye kan shahidan Karbala daidai yake da raya al’amarin Karbala. An ruwaito cewa, duk wanda ya zubar da hawaye, ko ya sa wasu suka yi kuka da bakin cikin abin da ya faru, sakamakonsa Aljanna ne. Wannan kuwa saboda duk wanda sa aka yi juyayin munanan abubuwan da suka faru a Karbala, to yana taimakawa ne wajen wanzuwar gwagwarmayar da Imam Husain (AS) ya somo ta, ta hanyar shahadarsa a falalen Karbala.

Wannan ne dalilin da ya sa ‘yan koren manyan azzaluman kasashen duniya a kullum suke kokarin hana irin wadannan tarurruka da muzaharori na Ashura. Sun yi cikakken nazarin yanayin kasashe, kuma sun gano cewa matukar al’umma suka ci gaba da raya irin ta’addancin da aka yi a Karbala, suka tashi suna fallasa zaluncin azzalumai tun na dauri, to ba kuwa za su cimma burinsu na danniya da babakere a kasashen musulmi ba.

Ba su san cewa zub da hawaye saboda Imam Husain (AS) na nufin wanzar da gwagwarmayarsa da tabbatar da cewa jama’a ‘yar kadan za ta iya mikewa tsaye don kau da danniya ba. Cikin abin da Imam Husain (AS) ya fada shi ne “Kowace rana Ashura ce, kowace kasa ma Karbala ce!” Abin da hakan ke nufi shi ne a ci gaba da wanzar da gwagwarmayarsa a ko’ina kuma a koyaushe. Wannan zance shi ne abin la’akarinmu a kullum. Kamar yadda Imam Husain (AS) ya mike ya ce A’A! ga zalunci, to dole a maimaita hakan a kullum, kuma wadannan tarurrukan juyayin dole su ci gaba da wanzar da wannan NA-KIN! Kada ‘ya’yanmu da matasanmu su dauka wannan wani al’amari ne na zaman makoki da kuka kawai. Su makiya Musulunci suna tsoron wadannan tarurrukan juyayin saboda kuka ne na goyon bayan wadanda aka zalunta. Kuma yin tir ne da kuma adawa da azzalumai.

Za mu yi amfani da wanan lokaci na juyayin, mu yi tir da Allah wadai da lafuffukan yaki da kasar Saudiyya da kawayenta suke tafkawa na kashe fararen hula a kasar Yemen da kuma shigen irin hakan da ke faruwa a Siriya, Iraq da Afghanistan. Muna kuma yin tir da munanan hare-haren da Yahudawan Sahayoniya suke kai wa kan al’ummar Palasdinu. Ba mu kuma yarda da haramtattun takunkuman da Shugaban Amurka, Trump yake ta faman kakaba wa jamhuriyar Musulunci ta Iran ba.

A nan Nijeriya Harkar Musulunci karkashin jagorancin Shaikh Ibraheem Yaqoub Zakzaky (H) ta kasance wacce ake zalunta, musamman a wannan gwamnatin da sauran gwamnatocin baya bisa umurnin kasashen waje. Irin kisan gillar da sojojin Nijeriya suka yi a Zariya tsakanin 12-14 ga Disamban 2015 ya yi kama kwabo da kwabo da irin mummunan ta’asar da aka yi wa Imam Husain, iyalinsa da mabiyansa a falalin Karbala.

A shekarar 2016 wata babbar kotun Tarayya da ke Abuja ta ba da umurnin a saki Jagoranmu, tana mai Allah wadai da tsare shin da ake yi, abin da ta ce ba a san shi a dokokin kasar nan da na kasashen duniya ba, amma gwamnatin Buhari ta kekasa kasa ta ki bin umurnin wannan kotun. Maimakon haka ma sai gwamnatin jihar Kaduna ta shigar da wata kara, inda ta kirkiro wasu tuhume-tuhume na wauta kan Jagoranmu Shaikh Ibraheem Zakzaky. To, ko a babbar kotun jihar Kaduna, an ba shi damar ya fita zuwa Indiya neman lafiya saboda tsanantar rashin lafiyarsa a kullum, amma gwamnatin sai da ta san yadda ta yi, ta kawo cikas ga tafiyar a watan da ya gabata.

Don haka a yayin da muke juyayin Ashura, muna kira ga gwamnatin Tarayya da ta saki Jagoranmu Shaikh Zakzaky, matarsa da daruruwan ‘yan’uwa musulmi maza da mata da take tsare da su tun Disamban 2015 tare da maido mana da hakkokinmu na ‘yan’adamtaka a duk fadin kasar nan.

SHAIKH ABDULHAMID BELLO
Muharram 10, 1441 (Satumba 09, 2019)